Gobara ta hallaka mahaifi da dansa a Kaduna

A shekaranjiya Laraba ne mazauna layin Kerawa da ke Tudun Wada Kaduna suka shiga cikin alhini da tashin hankali sakamakon rasuwa wani magidanci da dansa a wata gobara da ta kama gidansa.Wasu daga cikin makwabtansa sun ce wutar ta tashi ne a daya daga cikin dakunan gidan da misalin karfe 2:00 na daren Laraba.Wasu na […]

Gobara ta hallaka mahaifi da dansa a Kaduna
Gobara ta hallaka mahaifi da dansa a Kaduna

A shekaranjiya Laraba ne mazauna layin Kerawa da ke Tudun Wada Kaduna suka shiga cikin alhini da tashin hankali sakamakon rasuwa wani magidanci da dansa a wata gobara da ta kama gidansa.
Wasu daga cikin makwabtansa sun ce wutar ta tashi ne a daya daga cikin dakunan gidan da misalin karfe 2:00 na daren Laraba.
Wasu na zargin kawo wutar lantarki da aka yi da karfi ne ya janyo tashin gobarar wadda ta yi sanadin mutuwar maigidan mai kimanin shekara 48 mai suna Alhaji Isiyaku Basiru  da ke sayar da gwanjo a Kasuwar Barchi a Tudun Wada, Kaduna.
Marigayin dan Shugaban ’Yan Gwamjo na Kasuwar Barchi ne Alhaji Basiru.
daya daga cikin makwabtan marigayin wanda yana daga cikin wadanda suka fito da shi daga gidansa, amma bai ambaci sunansa ba, ya ce “Ina gida da misalin karfe 2:00 na dare sai na ji hayaniyar mutane, da na fito sai na tarar da wadansu mata biyar a kofar gidansa suna cewa wuta-wuta. Da zuwana  sai muka shiga cikin gidan bayan wani yaronsa ya samu damar bude mana kofar gidan. Ko da muka shiga cikin gidan hayaki ya turnuke ko’ina sai da na yi amfani da fitilar hannu domin haskawa. Daga nan ne muka hango Alhaji a kwance tare da mai dakinsa kusa da shi tana nunfasawa sama-sama.”
Ya kara da cewa: “Bayan mun dauko shi waje sai na ga ko motsi ba ya yi, daga nan ne na fahimci ba ya da rai. Sai  muka ci gaba da dukan kofofin dakunan gidan domin ceto sauran ’ya’yansa. Shi ma dansa dan shekara biyu ko da muka dauko shi ya riga ya rasu. Muna ganin sun rasu ne bayan sun shaki hayaki. Gaskiya mun ga tashin hankali sakamakon abin da ya faru ga marigayi Alhaji Isiyaku domin mutum ne mai taimakon na kasa da shi,” inji shi.
Wakilinmu ya samu bayanin cewa matarsa da sauran ’ya’yansa an garzaya da su asibitin Biba da ke Titin Matazu a Tudun Wada domin ceto rayukansu saboda shakar hayaki da suka yi.
Aminiya ta ziyarci gidan da abin ya faru inda ta tarar da makwabta da abokan arziki cikin alhini.
Abin mamaki da gidan shi ne babu wani wuri da ya kone illa cikin dakin da abin ya faru.
An yi jana’izarsa tare da dansa a makabartar Titin bashama da ke Tudun Wada da misalin karfe 9:00 na safe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.