Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno

Gobarar ta bazu cikin saura inda ta laƙume dukiya mai tarin yawa.

Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno

Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mandalari da ke Konduga a Jihar Borno, ta hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Gobarar, ta tashi da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, ta bazu zuwa yankunan da ke da cunkoson jama’a, inda ta cinye matsugunan wucin gadi da kuma kayayyaki masu tarin yawa.

Sojojin da aka jibge a Konduga, sun kai ɗauki nan take bayan samun labarin tashin wutar.

Sun haɗa kai da jami’an agaji da kuma al’ummar yankin domin shawo kan gobarar.

Duk da haka, akwai fargabar cewa yawan mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa.

Dakarun Operation Haɗin Kai da ke aiki a Konduga sun taka rawar gani wajen ceto mutane da kuma hana gobarar bazuwa.

“Sojoji sun kawo ɗauki cikin gaggawa, tare da tattara ma’aikata da kayan aiki don shawo kan gobarar da kare mutanen da lamarin ya shafa,” in ji wata majiya daga jami’an tsaro.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno, tare da haɗin gwiwar sojoji da hukumomin agaji, na ci gaba da ƙoƙarin shawo kan lamarin.

Hakazalika, an tura ƙungiyoyin lafiya domin kula da waɗanda suka jikkata.

Wannan ba shi ne karon farko da sansanin Mandalari ke fuskantar irin wannan iftila’i ba.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, tsakanin watan Fabrairu da Yunin shekarar 2024, gobara ta tashi aƙalla sau 43 a sansanin, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Shugaban al’ummar yankin, Bulama, ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro a Konduga, inda ya ce suna bayar da muhimmiyar gudunmawa ba kawai wajen magance rikice-rikice ba, har ma da tabbatar da tsaron ’yan gudun hijira.

“Muna godiya ga taimakon Allah SWT da nasu, domin ba don agajin sojoji ba, da lamarin zai iya yin muni matuƙa,” in ji shi.

A halin yanzu, hukumomi sun buƙaci ’yan gudun hijira da su ƙara yin taka-tsantsan domin hana sake faruwar irin wannan gobara, musamman a wannan lokaci na zafi.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), na ci gaba da rabon kayan tallafi, yayin da hukumomin tsaro suka tabbatar da cewa za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.