Gobara ta hallaka mutum biyu a Kasuwar Lemo ta Kaduna
Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Lemo da kayan marmari da ke tashar jirgin kasa a karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a ranarTalatar da ta wuce ta hallaka mutum biyu.Gobarar ta kuma lalata dukiya ta miliyoyin Naira tare da raunata mutum biyu da aka kai su asibitin Saint Geraild da ke Kakuri domin yi […]
Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Lemo da kayan marmari da ke tashar jirgin kasa a karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a ranarTalatar da ta wuce ta hallaka mutum biyu.
Gobarar ta kuma lalata dukiya ta miliyoyin Naira tare da raunata mutum biyu da aka kai su asibitin Saint Geraild da ke Kakuri domin yi masu magani.
Bayanai sun cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12:45 na dare ranar Litinin, kuma shaguna da dama suka kone, inda wasu suka dora alhakin tashin gobarar ne a kan wutar lantarki.
Aminiya ta samu labarin cewa mutum biyu da ake tsammanin sun mutu a kasuwar suna kwana ne a cikin shago lokacin da gobarar ta faru.
Wani mai suna Murkhtar Abdullah da ke zaune kusa da kasuwar, ya ce sun fara jin kaurin hayaki ne daga Layi na Bakwai da ke kasuwar kuma kafin su isa wurin shagon ya kama da wuta, inda ta watsu zuwa sauran shaguna kamar wutar daji.
An ce motocin kashe gobara na Hukumar ’Yan Kwana-Kwana ta Jihar Kaduna da na Kamfanin Barasa da ke Kakuri da na Matar Mai sun yi iya kokarinsu wajen kashe wutar.
Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufa’i ya kai ziyarar jaje ga ’yan kasuwar, inda ya ce gwamnati za ta gina kasuwar zamani a wurin. Ya ce ba don cushewar kasuwar ba da motocin kashe wuta sun samu shiga cikin sun kashe kafin ta yi varna.