Gobara ta hana dalibai rubuta jarabawa a Keffi
Hukumar gudanarwar Kwalejin Tarayya dake Keffi,Hedikwatar karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa ta ce baza ta gudanar da jarabawar zangon karatu na uku a makarantar ba sakamakon wata mummunar gobara da ta auku a gadajen kwanandalibai mata guda biyu a makarantar. A cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun shugaban makarantar, Babatunde danjuma, wanda aka […]
Hukumar gudanarwar Kwalejin Tarayya dake Keffi,Hedikwatar karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa ta ce baza ta gudanar da jarabawar zangon karatu na uku a makarantar ba sakamakon wata mummunar gobara da ta auku a gadajen kwanandalibai mata guda biyu a makarantar.
A cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun shugaban makarantar, Babatunde danjuma, wanda aka rabawa iyayen yara da manema labarai, hukumar makarantar ta bayyana cewa ta dage jarabawar zangon karatu na uku, wanda shine na karshe da daliban ke rubutawa don shiga aji na gaba a makarantan ne sai bayan an kammala sake ginin gidajen kwanan da lamarin ya shafa.
Sanarwar ta bayyana cewa gobarar ta faro ne da daddaren ranar Lahadi da misalin karfe 9 zuwa wayewar garin Litinin 27 ga watan Nuwambanr 2017, kafin daga bisani jami’an hukumar kashe gobara suka iso suka kashe. Sanarwar ta cigaba da bayyana cewa kodayake gobarar ta kune gidajen kwanan matan biyu kurmus, amma babu wata daliba kodalibi ko wani daban daya rasa ransa sakamakon lamarin. Sai dai sanarwar bata bayyana musababbin gobarar ba.
Daganansai aka bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar tsofaffin daliban makarantar da masu hannu da shuni su kawo wa kwalejin dauki, ta yadda za a sake gina musu gidajen kwanan dalibai mata, wadanda acewar sanarwar kowannensa ke dauke da dakuna 30 da lamarin ya shafa cikin gaggawa, don bai wa daliban damar komawa makaranta su cigaba da karatu.
Da wakilinmu ya tuntubi shugaban kwalejin, Babatunde danjuma ta waya don jin ta bakinsa akan musabbabin gobarar ya bayyana cewa,‘har zuwa lokaci da aka hada wannan labari hukumar kwalejin da hukumar kashe gobara ta shiyar karamar Hukumar Keffi da suka kashe gobarar basu gano abinda ya haifar da gobarar ba.
Ya ce ananan ana cigaba da gudanar da bincike, inda ya yi alkawari sanar da wakilinmu da zarar sakamakon binciken ya fito.