Gobara ta jikkata mutum 38 a hedikwatar ‘yan sandan Masar

Mutum 38 sun jikkata a wata gobara da ta tashi a hedikwatar ’yan sandan kasar da ke yankin Ismailia

Gobara ta jikkata mutum 38 a hedikwatar ‘yan sandan Masar

Mutum 38 sun jikkata a sakamakon a wata gobara da ta tashi a babban ofishin rundunar ’yan sandan kasar da ke yankin Ismailia.

Ma’aikatar Lafiyar kasar ta ce an garzaya da wadanda suka samu raunukan zuwa asibitoci, wasu kuma ana kula da su bayan an ceto su daga cikin inda aka girke motoci 50 na daukar marasa lafiya.

Bayan awanni ana aikin ceto, an yi nasarar shawo kan gobarar, wadda ta tashi gabanin asubahin ranar Litinin, a yayin da ginin ke cike da jami’an ’yan sanda.

Ko da yake gwamnatin kasar ba ta bayyana adadin jami’ai da tsararrun da ke wurin a lokacin da gobarar ta tashi ba.

Hotuna gobarar da aka yada a kafofin sada zumunta sun nuna yadda mutanen suka makale a cikin ginin da gobarar ta kama suke kururuwar neman agaji, a yayin da ake ci gaba da aikin ceto

Gobarar ta lakume ginin gaba daya, kafin daga bisani a samu nasarar hana ta yaduwa zuwa sauran wurare. Ma’aikatar lafiyar ta ce kawo yanzu babu bayani game da ko an samu asarar rai.

Ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma jami’an tsaro sun killace wurin ana ci gaba da aikin ceto.

Mininstan harkokin cikin gidan kasar, Mahmoud Tawfik ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, tare da yin inganta tsarin tsaro a hedikwtar ’yan sandan.