Gobara ta kama a Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Ya zuwa yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

Gobara ta kama a Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Gobara a Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta kama da wuta a safiyar wannan Litinin din.

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musababbin tashin gobarar ba.

Darektan Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Salau Ozigi ne ya tabbatar da faruwar hakan, yana mai cewa gobarar ba ta tsallaka cikin farfajiyar zaauren majalisar ba.

Kakakin Majalisar, Prince Mathew Kolawole, ya alakanta faruwar gobarar da sakaci, yana mai cewa jami’an tsaro za su gudanar da bincike a kan lamarin.

Kazalika, ya ce wannan ibtila’i ba zai kawo wa majalisar wani koma baya ba wajen ci gaba da sauke nauyin da rataya a wuyanta.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya

Tags