Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 na asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da sauran kayayyaki.

Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira

Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar.

A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki.

Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun yi nasarar shawo kan gobarar da ƙyar da jibin goshi bayan da ta yi ɓarna mai yawan gaske.

Tuni dai aka yi wa marigayin jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya shimfiɗa.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar (SEMA) da sauran hukumomin jin ƙai sun baza jami’ansu a sansanonin don daidaita lamarin.