Gobara ta kashe mutum 100 a wajen bikin aure a Iraƙi

Sama da mutum 150 kuma sun ji raunuka sanadin gobarar

Gobara ta kashe mutum 100 a wajen bikin aure a Iraƙi

Wata gobara da ta tashi a wani dakin taro ta kashe mahalarta bikin aure sama da 100 sannan ta jikkata sama da 150 a birnin Hamdaniyah na kasar Iraƙi.

Kafafen yada labarai da hukumomin lafiyar kasar ne suka tabbatar da alkaluman da sanyin safiyar Laraba.

Hukumomin lafiya a lardin Ninevah sun ce “mun kirga gawarwaki 100 ya zuwa yanzu a gobarar da ta tashi a dakin biki a Hamdaniyah, sama da 150 kuma sun jikkata,” kamar yadda kamfanin dillancin Iraƙi (INA) ya rawaito ta bakin Ma’ailatar Lafiyar kasar.

A babban asibitin garin na Hamdaniyah, wanda galibin mazaunansa Kiristoci ne da ke Gabashin Mosul, wani mai ɗaukar hoton Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya ce ya ga motocin daukar marasa lafiya da dama na isa wajen, yayin da mutane da dama suka yi wa wajen kawanya suna bayar da gudummawar jini.

Kazalika, an ga wasu mutane na taruwa a kofofin wata mota da ta dauko sassan jikin gawawakin da suka kone.

A cikin wata sanarwa, hukumar tsaron Sibil Difens ta kasar ta ce, “akwai abubuwa masu barazanar konewa a wajen da ba sa bin ka’idar dokokin kashe gobara.

“Gobarar ta sa wasu ɓangarori na rufin ginin ya faɗo saboda zafin wutar da kuma rashin ingancin kayan da aka yi ginin da shi.

“Binciken farko-farko ya nuna an yi amfani da tartsatsin wuta a wajen bikin, wanda hakan ne ya haifar da tashin gobarar,” in ji hukumar ta Sibil Difens.