Gobara ta kashe mutum 27 a wata mashaya a Bangkok
Thailand ta sha fuskantar suka kan yadda ake aiwatar da ƙa’idojin lafiya da tsaro a mashaya da wuraren shaƙatawa.
Aƙalla mutum 27 sun mutu, yayin da wasu 63 suka jikkata sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wata mashaya da gidan cin abinci a birnin Bangkok na ƙasar Thailand.
Gobarar ta tashi ne da daddaren Lahadi a mashayar Rong Beer Na Lat Phrao da ke wajen birnin Bangkok, inda shaidu suka ce mutane sun riƙa guje-guje cikin firgici yayin da wuta ta mamaye ƙofar shiga ginin.
- Farashin mai ya ƙara tashi dalilin rikicin Amurka da Iran
- Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin jarabawar WAEC da NECO
Gwamnan Bangkok, Chadchart Sittipunt, ya ce gobarar ta bazu har zuwa saman rufin ginin, yana mai bayyana cewa hayaƙi ne ya fi haddasa mace-macen.
Ya ƙara da cewa mutum 63 na samun kulawa a asibiti, ciki har da 22 da ke cikin mawuyacin hali, yayin da hukumomi suka soma bincike kan musabbabin gobarar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin gawarwakin an same su ne kusa da hanyar fita ta gaggawa, wadda ake zargin ta toshe a lokacin da gobarar ta tashi.
Wani direban babur mai suna Surin Jaiharn ya ce ya taimaka wajen ceto kusan mutum biyar da jikinsu ya ƙone bayan ya ga wutar na fita ta ƙofar mashayar.
Ya ce ya yi amfani da zane wajen kashe wutar da ke jikinsu, yayin da wani direban babur ya taimaka wajen fitar da wata mata daga wurin.
Hukumomi sun ce zuwa safiyar Litinin sun tantance mutum 10 daga cikin waɗanda suka mutu, inda tara ’yan ƙasar Thailand ne, ɗaya kuma ɗan ƙasar Laos.
Firaministan Thailand, Anutin Charnvirakul, wanda ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, ya ce mashayar tana da lasisin aiki a matsayin gidan cin abinci, kuma ana binciken ko an bi matakan da suka dace afin afkuwar gobarar.
Ya kuma tabbatar da cewa za a ɗauki matakin doka kan duk wanda bincike ya nuna ya karya ƙa’idojin lafiya da tsaro.
Binciken farko ya nuna cewa akwai wasu sassan ginin da ba su da hanyoyin fita na gaggawa a fili, lamarin da ake zargin ya ƙara tsananta asarar rayuka.
Gobarar ita ce mafi muni a Thailand tun bayan gobarar da ta tashi a gidan rawa na Santika Club da ke Bangkok a daren sabuwar shekara ta 2009, wadda ta kashe mutum 67 tare da jikkata sama da 200.
Thailand ta sha fuskantar suka kan yadda ake aiwatar da ƙa’idojin lafiya da tsaro a mashaya da wuraren shaƙatawa.
A shekarar 2022 ma, wata gobara ta kashe mutum 25 a Mountain B da ke lardin Chonburi.