Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe
Gwamnatin ta yi alƙawarin tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.

Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025.
Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba.
- Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas
- Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq
Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar.
Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa kan asarar da suka yi.
Domin magance matsalar, hukumar YOSEMA ta fara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kauce wa gobara.
Haka kuma, sun kafa kwamitoci da za su taimaka wajen kare lafiyar al’umma, musamman a lokacin rani da hunturu.
Dokta Goje ya ce hukumar, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar, za su ɗauki matakan hana ƙone daji da kuma bin ƙa’idojin zubar da shara domin rage haɗuran gobara.
A gefe guda, Gwamna Mai Mala Buni ya umarci hukumar YOSEMA da ta tantance ɓarnar da gobarar ta yi, domin sanin irin taimakon da waɗanda lamarin ya shafa suke buƙata.
Gwamnan ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa za a tallafa musu.
A halin yanzu, hukumomi na ci gaba da faɗakar da jama’a kan muhimmancin kiyaye dokokin kare gobara domin gujewa aukuwar irin wannan iftila’i a gaba.