Gobara ta kona ofisoshi 5 na gidan Rediyon Freedom a Kaduna
A tsakiyar daren ranar Lahadin nan ne wata gobara to kona ofisoshi biyar a gidan rediyon Freedom na jihar Kaduna. Aminiya ta fahimce cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 2:30 na dare kuma babu wanda ya san abin da ya yi sanadin tashin gobara janyota. Ofishin da abin ya shafa sun hada da: […]
A tsakiyar daren ranar Lahadin nan ne wata gobara to kona ofisoshi biyar a gidan rediyon Freedom na jihar Kaduna.
Aminiya ta fahimce cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 2:30 na dare kuma babu wanda ya san abin da ya yi sanadin tashin gobara janyota.
Ofishin da abin ya shafa sun hada da: sashen Injiya da ofishin shugaban kasuwanci da dakin taro da ofishin mai gadi sannan da dakin direbobi gidan.
Shugaban sashen aiyuka na gidan rediyon watau { Head Operations) Abubakar Jiddah Usman ya tabbatarwa da wakilinmu aukuwar lamarin.

Ya ce, babu wanda yasan abin da ya janyo gobarar, amma akwai alamun matsalar wutar lantarki ne tun da gobarar ta faro ne daga sashen wutar lantarki na gidan.
Ya ce, gidan zai ci gaba da yada shirye shiryensu duk da cewa sun dan dakata na wasu sa’o’i amma sun dawo aiki.