Gobara ta kone alluran rigakafi miliyan 2 a Gombe
Gobarar ta tashi da sanyin safiyar ranar Litinin.
Gobara ta tashi a babban dakin ajiye magunguna na Jihar Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar alluran rigakafin cutar shan-inna da sankarau sama da miliyan biyu.
Gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda aka yi hasashen asarar Naira biliyan biyar a sanadin gobarar.
Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ziyarci wajen don ganewa idonsa irin barnar da gobarar ta yi.
Gwamnan ya umarci a gudanar da bincike game da musabbabin tashin wutar don gujewa faruwar hakan a gaba.
Ya ce kayayyakin kula da kananan yara da mata masu juna biyu da kuma kwalaben alluran rigakafi sama da miliyan biyu ne, suka salwanta sakamakon tashin gobarar.
“Na umarci Hukumar Kashe Gobara da su binciko musabbabin tashin gobarar don daukar matakin kare sake faruwar hakan a gaba.
“Duk da haka mun umarci masu ruwa da tsaki musamman na kasashen waje irin su UNICEF da WHO da sauransu da su shigo tunbda tuni anbyi zangon farko.
“Muna bukatar alluran rigakafi saboda gudun barkewar Kwalara.”