Gobara ta kone dakin daliban Sakandaren Sojan Ruwa a Kalaba
Tangardar da ake zargin ta wutar lantarki ce da aka samu a Makarantar Sakandare ta Sojan Ruwa da ke Akpabuyo, Jihar Kuros Riba a ranar Talatar makon jiya ta jawo gobara mai tsanani har daya daga cikin dakunan kwanan daliban da ke kusa da turken wutar lantarkin ya kama da wuta. Da misalin karfe 11 […]
Tangardar da ake zargin ta wutar lantarki ce da aka samu a Makarantar Sakandare ta Sojan Ruwa da ke Akpabuyo, Jihar Kuros Riba a ranar Talatar makon jiya ta jawo gobara mai tsanani har daya daga cikin dakunan kwanan daliban da ke kusa da turken wutar lantarkin ya kama da wuta. Da misalin karfe 11 na ranar Talata ce wutar ta kama bayan da kamfanin rarraba wutar lantarki ya dawo wa makarantar da wuta.
Makarantar mai dalibai sama da 200 duk sun tsira ba tare da samun rasa rayuka ba.
Jim kadan da samun labarin gobarar wakilinmu ya garzaya kauyen Akpabuyo wanda bai da nisa daga Kalaba domin gane wa idonsa abin da ya faru, kuma ya iske Kwamandar makarantar O.A. Kudairi tana famar taimaka wa jami’an kashe gobara da suka zo don kashe wutar.
Wani daga cikin daliban makarantar da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, “Gobarar ta tashi ne a unguwar da ake kira Adeniyi Hall wato ‘Blue House.’ Da ganin gobarar ta tashi kowannenmu muka shiga kiran iyayenmu muna sanar musu halin da ake ciki inda suka rika zuwa suna gani.”
Aminiya ta gano wadansu daga cikin daliban makarantar sun riga sun gama jarrabawa sauran ’yan ajin karamar sakandare, aji uku da kuma na babban aji su ma aji na uku.
Iyayen da suka zo makarantar wadansu sun tafi da ’ya’yansu da suka gama jarrabawa zuwa gida yayin da ake sa ran wadanda ba su gama tasu jarrabawar ba za su ci gaba da zama a makarantar.