Gobara ta kone dakin kwanan dalibai a makarantar ‘yan mata ta Guri
Gobara ta kone dakunan kwa-nan dalibai mata a karamar sakandaren gwamnati ta Guri da ke Jihar Jigawa a ranar Litinin da ta gabata.Gobarar da ba a san musabbabin faruwarta ba, sai dai jami’an makarantar sun ce suna bincike domin gano masababbabinta.Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya wato sibil difens Alhaji Muhammed Gidado ya tabbatar da […]

Gobara ta kone dakunan kwa-nan dalibai mata a karamar sakandaren gwamnati ta Guri da ke Jihar Jigawa a ranar Litinin da ta gabata.
Gobarar da ba a san musabbabin faruwarta ba, sai dai jami’an makarantar sun ce suna bincike domin gano masababbabinta.
Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya wato sibil difens Alhaji Muhammed Gidado ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce goabar ta kone daukacin dakin da ake kira Peace kurmus kuma ko allura ba cire ba.
Ya kara da cewa wutar ta fara barna tun kimanin karfe 4:00 na dare har zuwa karfe 6:00 na safe ba ta daina ci ba. Ya ce akwai matsalar waya a yankin Guri shi ya sa ba a samu sanar da jami’an kwana-kwana cikin hanzari ba har sai da wutar ta cinye dakin.
Bayanai sun ce babu wanda ya samu rauni a cikin daliban makaranatar.