Gobara ta kone dakunan kwanan daliban Kwalejin ’Yan Mata ta Kazaure
Gobara ta kone wasu dakunan kwanan dalibai a Kwalejin’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Kazaure a Jihar Jigawa.Gobarar wadda ta dauki tsawon awa daya tana ci ba tare da an shawo kanta ba ta kone gadaje da kayan kwanciyar dalibai da na karatu na miliyoyin NairaKwamandan Hukumar Tsaro ta Farar Hula a Jihar Jigawa […]
Gobara ta kone wasu dakunan kwanan dalibai a Kwalejin’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Kazaure a Jihar Jigawa.
Gobarar wadda ta dauki tsawon awa daya tana ci ba tare da an shawo kanta ba ta kone gadaje da kayan kwanciyar dalibai da na karatu na miliyoyin Naira
Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farar Hula a Jihar Jigawa Alhaji Muhammed Gidado wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce da taimakon jami’an tsaro aka samu ceto daliban daga gobarar.
Ya ce har zuwa lokacin hukumarsa da hukumar kashe gobara ta jihar ba su gano dalilin tashin gobarar ba.
Sai dai wasu mutane a cikin gari suna baza jita-jitar cewa gobarar ta tashi ne sakamakon girki da daliban suke yi da risho a dakunansu, wasu kuma sun ce wai waya ce aka sa caji ta kone.
Kwamandan ya gargadi jama’a su yi kaffa-kaffa wajen amfani da wuta musamman a wannan lokaci na sanyi.