Gobara ta kone gidaje 10 da kayan abincin Naira miliyan 5 a Jigawa
Rahotanni daga Karamar Hukumar Suletankarkar da ke jihar Jigawa na cewa, wata gobara ta kone gidajen ajiye abinci 10 a kauyen Dirani da ke jihar. Jami’in Karamar Hukumar Alhaji Usman Abubakar, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN ranar Litinin cewa, gobarar ta kone hatsi da ya kai na Naira miliyan 5. Alhaji Usman, ya ce […]
Rahotanni daga Karamar Hukumar Suletankarkar da ke jihar Jigawa na cewa, wata gobara ta kone gidajen ajiye abinci 10 a kauyen Dirani da ke jihar.
Jami’in Karamar Hukumar Alhaji Usman Abubakar, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN ranar Litinin cewa, gobarar ta kone hatsi da ya kai na Naira miliyan 5.
Alhaji Usman, ya ce gobarar ta cinye hatsi kamar: dawa, wake, gero da sauran hatsi. Gobarar ta fara ne daga wani dakin dafa abinci ranar Lahadi.