Gobara ta kone gidaje 1,000 a unguwar takalawa a Malaysia

A cewar hukumar, dukkan gidaje na wucin gadi da suka kai fadin kadada 10 sun ƙone kurmus. Sai dai ba a samu rahoton mutuwa ko rauni ba

Gobara ta kone gidaje 1,000 a unguwar takalawa a Malaysia

Akalla gidaje 1,00o ne suka kone, a yayin da dubban mutane suka rasa muhallansu bayan tashin gobara a safiyar Lahadi a Jihar Sabah da ke kasar Malaysia.

Hukumomin kasar sun bayyana cewa dukkan gidaje na wucin gadi da suka kai fadin kadada 10 sun ƙone kurmus bayan tashin gobarar a wata unguwar talakawa da ke garin Sandakan.

Gidajen da suka kone yawancinsu an gina su ne na katako, a yankin mai cike da talakawa ’yan asalin ƙasar da kuma al’ummomin da ba su da takardun zama.

Kwamishinan ’yan sanda na Sandakan, George Abd Rakman, ya bayyana cewa wannan “babbar masifa mai tayar da hankali” ta shafi fiye da mutane 9,000.

Hukumar kashe gobara ta Sabah ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:32 na safe, inda ta tura ma’aikata 37 daga ofisoshi biyu domin shawo kan gobarar.

Amma da haka, ƙuntataccen hanya ya hana motocin kashe gobara isa wurin, sannan ƙarancin ruwa da iska mai ƙarfi suka ƙara haddasa bazuwar wutar.

A cewar hukumar, dukkan gidaje na wucin gadi da suka kai fadin kadada 10 sun ƙone kurmus. Sai dai ba a samu rahoton mutuwa ko rauni ba.

Firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, ya ce gwamnatin tarayya na aiki tare da hukumomin Sabah domin samar da agajin gaggawa da matsuguni na wucin gadi ga waɗanda abin ya shafa.

Ya jaddada cewa “abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne tsaron rayukan jama’a da kuma taimakon gaggawa a wurin da abin ya faru.