Gobara ta kone gidaje fiye da talatin a kauyen Usuk-utang
Kadara ta sama da Naira miliyan biyu da rabi ta kone kurmus a kauyen Usuk-utang da ke harabar hukumar hada-hadar jiragen ruwa ta Nijeriya, a yankin karamar Hukumar Birnin Kalaba da Jihar Kuros Riba, a makon da ya shige.A kauyen ne dai da yawa daga ’yan asalin Arewa ke gudanar da hada-hadar kasuwancinsu. Gobarar ta […]
Kadara ta sama da Naira miliyan biyu da rabi ta kone kurmus a kauyen Usuk-utang da ke harabar hukumar hada-hadar jiragen ruwa ta Nijeriya, a yankin karamar Hukumar Birnin Kalaba da Jihar Kuros Riba, a makon da ya shige.
A kauyen ne dai da yawa daga ’yan asalin Arewa ke gudanar da hada-hadar kasuwancinsu. Gobarar ta tashi ne a sanadiyyar tartsatsin wutar lantarki, kamar yadda mazaune kauyen ka zato a Larabar makon jiha.
An kiyasta gidaje da suka kone sun kai sama da talatin, yayin da shaguna guda bakwai, wadanda aka ce kaya da cinikin da aka yi aka bari a cikinsu sun kai na sama da Naira dubu dari bakwai, su ma sun kone kurmus.
Alhaji Ibrahim Altine, shugaban ’yan kasuwar mazauna unguwar, wanda shi ma shagonsa da gidansa da cinikin da ya yi a ranar, duk wutar ba ta bar masa komai ba ne ya shaida wa Aminiya haka a lokacin da ta ziyarci wurin don gane wa ido irin ta’adin da gobarar ta yi.
Ya ce misalin karfe uku na dare ne wutar ta kama unguwar, “Yayin da na ga wani haske ya cika sama, ga hayaki na tashi, sai na ji mutane suna ihu suna cewa ‘jama’a ku fito gobara’. Ba mu san musabbabin gobarar ba, amma muna kyautata zato tartsatsin wutar lantarki ne ya haifar da haka don a lokacin akwai wuta”.
Ya kara da cewa sun yi iyakacin bakin kokarinsu wajen kashe wutar, amma da taimakon Allah, sannan da na jama’a da kuma jami’an kashe gobara aka muka kira, aka samu shawo kan matsalar”.
Har wa yau ya ce, “Dukiya da kadarori da suka kone, ciki har da shagona da gidana da cinikin da na yi Naira dubu dari bakwai, duk wutar ta lashe su, gidaje kuwa sun fi sama da talatin da suka kone”.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci unguwar ya iske wadanda balahirar ta afka mawa da ya zanta da su, suka tabbatar masa da afkuwar lamarin, suna ta kokarin gyara matsuguni da wurin neman abincinsu.