Gobara ta kone sansanin ’yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh
Sansanin na kunshe da mutane fiye da miliyan daya.
Wata gobara ta kone sansanin ’yan gudun hijirar Rohingya da ke kasar Bangladesh, lamarin da ya bar dubban ’yan gudun hijirar babu matsugunni.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sansanin ’yan gudun hijirar wanda shi ne ya fi kowanne yawan mutane fiye da miliyan daya, na kunshe da mutanen da mafi yawan su Musulmi ne da aka bude shi tun 2017, lokacin da yakin yankin ya ta’azzara.
- Ganduje ya shirya wa zaben Kano makarkashiya —NNPP
- Na ji dadin raga-raga da muka yi wa United —Klopp
Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Bangladesh, sun ce kawo yanzu an fara shawo kan wutar, amma dai ba a ma kai ga fara binciken musababbin tashin ta ba.
Bayanai sun ce kafin zuwan jami’an kashe gobara, sai da ’yan gudun hijirar suka fara yunkurin kashe gobarar, amma duk da haka ta yi matukar barna.