Gobara ta kone shaguna 10 a Kasuwar Rimi da ke Kano
Gobarar ta tashe ne sanadin tartsatsin wutar lantarki
Wata gobara da ta tashi cikin dare ta kone shaguna 10 a Kasuwar Rimi da ke birnin Kano.
A cewar Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 8:40 na daren Laraba.
- Sabuwar cuta ta kashe mutum 4, wasu 10 sun kwanta a asibitin Kafanchan
- Zaɓin Ganduje lalata tsarin APC ne – Salihu Lukman
Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga wani mai suna Magaji Umar, cewa gobara ta tashi a kasuwar, bangaren da suke sayar da katifu da gadaje da kuma kayayyakin kafinta.
“Da samun rahoton, sai muka tura jami’anmu na kwana-kwana wajen, kuma suka isa wajen da misalin karfe 8:49, domin su kashe ta, ta yadda ba za ta ci gaba da kone shagunan ba,” in ji asanarwar.
Saminu ya kuma ce shaguna shida da wasu rumfunan wucin gadi hudu sun kone kurmus, sai wani gidan wanka da shi ma wutar ta dan taba shi.
Ya ce wani tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa gobarar, amma ya ce suna kan bincike don gano hakikanin gaskiyar hakan.
Sai dai Kakakin ya ce ba a sami rahoton asarar rai ko jin rauni ba, amma ya shawarci ’yan kasuwa da su tabbatar suna kashe dukkan kayan lantarki kafin su bar shagunansu a kullum. (NAN)