Gobara ta kone shaguna 41 a kasuwar Kurmi da ke Kano

Gobarar dai ta tashi ne a bangaren ‘yan littattafai na kasuwar.

Gobara ta kone shaguna 41 a kasuwar Kurmi da ke Kano

Wata gobara (tsohuwar ajiya)

Akalla shaguna 41 ne suka kone bayan tashin wata gobara a Kasuwar Kurmi da ke Kano da sanyin safiyar ranar Litinin.

Ana ganin kasuwar dai a matsayin wacce ta fi dadewa a birnin Kano, cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya.

Gobarar, wacce ta fara wajen misalin karfe 01:00 na dare, ta shafi shagunan da ke bangaren ’yan littattafai ne na kasuwar.

A cewar Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, “Mun samu rahoton gobarar ne daga wani Malam Baba Nasidi da misalin karfe 01:58, a bangaren ’yan littattafai na kasuwar.

“Da jin haka ba mu yi wata wata ba muka aike da ’yan kwana-kwana wajen da misalin karfe 02:07, inda muka samu nasarar kashe ta,” inji shi.

Kakakin ya kuma ce akalla shagunan wucin gadi 37 ne suka kone, sai kuma wasu ginannun shaguna guda hudu da su ma gobarar ta shafa sama-sama.

Ya ce tangardar wutar lantarki ce ta haifar da gobarar.

Daga nan sai ya shawarci ’yan kasuwa da su tabbata suna kashe dukkan kayayyakin wutar lantarki kafin su bar shagunansu a kullum.