Gobara ta kone shaguna 50 a kasuwar ’yan Katako a Kano

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin.

Gobara ta kone shaguna 50 a kasuwar ’yan Katako a Kano

Sama da shaguna 50 ne suka kone kurmus sannan dukiyar miliyoyin Naira ta lalace a wata gobara da ta tashi a kasuwar ’yan Katako da ke unguwar Rijiyar Lemu a Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Shugaban kasuwar, Mamuda Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin.

Ya ce shagunan da gobarar ta shafa na da katako, injin feshi, kujeru, da sauran kayan aikin kafinta a cikin su.

Sai dai ya yaba wa jami’an Hukumar Kashe Gobara ta jihar, bisa kai dauki a kan lokaci da suka yi zuwa kasuwr.

Kazalika, ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su tallafa wa ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyarsu.

Har wa yau, kakakin hukumar kashe gobara na jihar, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kara da cewa gobarar ta kone kimanin shaguna 25 gaba daya, yayin da wasu shaguna da dama gobarar ba ta kone su gaba daya ba.

“Mun samu kiran waya da misalin karfe 1 na safe kuma mutanenmu sun samu nasarar kashe wutar da misalin karfe 2 na safe,” in ji Abdullahi.

Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe

Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa

’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara