Gobara ta kone shaguna 70 a kasuwar Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, gobara ta lakume shagunan wucin gadi 70 a kasuwar ‘Yan Katako dake unguwar Rijiyar Lemo a jihar Kano. Kakakin hukumar Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN hakan yau a Kano. Alhaji Saidu, ya ce shaguna 30 sun kone kurmus yayin da sauran 40 […]
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, gobara ta lakume shagunan wucin gadi 70 a kasuwar ‘Yan Katako dake unguwar Rijiyar Lemo a jihar Kano.
Kakakin hukumar Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN hakan yau a Kano.
Alhaji Saidu, ya ce shaguna 30 sun kone kurmus yayin da sauran 40 wasu kayan cikin shagunan ne suka kone.
Hukumar kashe gobarar ta ce, sun samu sanarwar tashin gobarar ne daga wani mai suna Bashir Suleiman da misalin karfe 3:45 na asubahin yau Alhamis.