Gobara ta kone shaguna a tsohuwar kasuwar Sakkwato

Shaguna da yawa ne suka kone, aka samu dimbin asara, sanadiyar gobara da ta tashi a tsohuwar kasuwar Sakkwato da ke cikin birnin jihar a Asabar da ta gabata. Bayan asarar kayan abinci da na masarufi na miliyoyin Naira da aka yi, ba a samu asarar rayuwa ko jikata ba. Duk da ba a san […]

Gobara ta kone shaguna a tsohuwar kasuwar Sakkwato

Shaguna da yawa ne suka kone, aka samu dimbin asara, sanadiyar gobara da ta tashi a tsohuwar kasuwar Sakkwato da ke cikin birnin jihar a Asabar da ta gabata.

Bayan asarar kayan abinci da na masarufi na miliyoyin Naira da aka yi, ba a samu asarar rayuwa ko jikata ba.

Duk da ba a san abin da ya yi sanadin tashin wutar ba, Mataimakin shugaban kungiyar ’yan kasuwar, Alhaji Almustapha Ladan ya yi kira ga hukuma da kungiyoyi da daidaikun jama’a da su taimaki ’yan kasuwar da abin ya shafa.

Kwamishinan al’amuran cikin gida, Alhaji Isah Sadik Achida, wanda yake nan lokacin da wutar ke ci; ya jinjina wa Kwamishinan ’yan sanda da ya zo wurin da kansa don gane wa idonsa abin da ke faruwa. Hakan ya sanya bata gari ba su samu yadda suke so ba.

Haka ma Sanata Aliyu Wamakko ya jajanta wa wadanda gobarar ta shafa; a wata takarda da mai magana da yawunsa, Malam Bashir Mani ya sa wa hannu. Ya nuna rashin jin dadinsa, inda ya yi fatar za a taimaka wa mutanen da suka samu asara.

A watan Afirilun da ya gabata na bana ma, an samu irin wannan gobarar a daya bangaren kasuwar da ake kira tashar Kyame. Sai kuma wannan a yanzu da ta tashi a kan titin Ahmadu Bello da aka samu nasarar ciwo kanta nan take ba tare da ta tsallaka zuwa sauran bangarorin kasuwar; wanda mutanen gari da masu shagunan da jami’an kwana-kwana suka hada hannu wajen dakile gobarar.