Gobara ta lakume dimbin dukiya a Kano
A safiyar Litinin da ta gabata ne wata gobara ta tashi a Kasuwar ’Yan Tsantsi da ke bakin Asibitin Murtala, kusa da Bankin Unity da ke birnin Kano. Gobarar, wacce ake kyautata zaton ta tashi ne sakamkaon matsala da aka samu daga wutar lantarki, ta lashe sama da shaguna biyar da kuma sama da akwaku 70. […]
A safiyar Litinin da ta gabata ne wata gobara ta tashi a Kasuwar ’Yan Tsantsi da ke bakin Asibitin Murtala, kusa da Bankin Unity da ke birnin Kano.
Gobarar, wacce ake kyautata zaton ta tashi ne sakamkaon matsala da aka samu daga wutar lantarki, ta lashe sama da shaguna biyar da kuma sama da akwaku 70. Haka kuma an bayyana cewa an samu nasarar kashe wutar ne ta hanyar taimakon jama’ar gari da kuma jam’an kwana-kwana da na ’yan sanda.
Malam Auwal Abdullahi shi ne shugaban kasuwar, ya bayyana wa Aminiya cewa gobarar ta jawo asara ta miliyoyin Naira. “Mun wayi gari da wannan musiba wacce ta cinye kusan rabin kasuwarmu tare da makwabtanmu masu shaguna. Muna tuba ga Ubangiji a kan wannan ibtila’i da Ya jarrabe mu da shi.” Inji shugaban.
Shi ma wani dan kasuwa wanda wannan gobara ta hada da kayansa mai suna Hafizu, ya bayyana asarar da suka yi tare da rokon gwamnati da ta kawo musu agaji. “Ni kaina kayan da ke shagona, wanda nake sayar da kayan kwalliyar mata, duk sun tafi a wannan gobarar, don haka muke rokon gwamnati da sauran al’ummar gari masu hali da su kawo mana dauki, domin mu koma mu ci gaba da gudanar da sana’armu, kasancewar mafi yawa daga cikinmu ba mu da wani kudin da za mu sake yin jari da su. Don Allah gwamnati ta taimaka mana” Inji shi.
Aminiya ta tuntubi Shugaban sashen ayyuka na Hukumar Kwana-kwana, Alhaji Kassim Musa inda ya bayyana cewa har yanzu hukumarsu na nan na binciken sanadin tashin gobarar.