Gobara ta lakume dukiya a kasuwar Kalaba

  Dukiya da kadarori ta milyoyin nairori ce aka yi asara a wata gobara da ta tashi da daddaren Litinin da ta gabata da misalin karfe tara na dare a kasuwar Watt, kasuwa mafi girma da ke Kalaba duk da babu wanda ya  iya tantance sanadin tashin gobarar bayan  “yan kasuwar sun rufe shaguna sun […]

Gobara ta lakume dukiya a kasuwar Kalaba

 

Dukiya da kadarori ta milyoyin nairori ce aka yi asara a wata gobara da ta tashi da daddaren Litinin da ta gabata da misalin karfe tara na dare a kasuwar Watt, kasuwa mafi girma da ke Kalaba duk da babu wanda ya  iya tantance sanadin tashin gobarar bayan  “yan kasuwar sun rufe shaguna sun tafi gidajen su ,yan kasuwa  da  daman gaske ne suka tafka asara ta dukiya a wannan kasuwa kafin jami’an kashe gobarar su zo da kuma dimbin mutanen da suka kawo gudunmawa don kashe gobarar da kuma  kare dukiyoyin jama,a ne sukayi ta bakin   kokari kafin daga bisani jami’an kashe gobara suka zo  aka ci galabar wutar aka kashe ta .

Sashen da wutar tafi yin barna shi ne sashen masu sayar da kayan lantarki da gyaran kwamfuta da kuma sauran kayayyakin lantarki da ke gefen layin Hewett sune suka fi tafka asara.

Olumide Sorumo wani da ke sana’ar sayar da kayan kwamfuta ya tafka asara, ya shaida wa Aminiya cewa wutar ta kama ne jim kadan da ’yan kasuwar suka rufe shagunan su suka tafi gidajen su.

 “Mu dai hayaki muka fara gani ya turnuke sama daga bisani sai muka ga harshen wuta tsakanin shagunan mutane yana tashi”inji shi.

Wakilinmu ya leka kasuwar inda ake sayar da amsa kuwwa (lasifikoki), kwamfutoci, da kuma sauran kayayyakin lantarki da aka fi sani da suna layin Yarabawa.

A zantawar wakilinmu da Alhaji Rauf Muhammad shugaban sashen ’yan kasuwar, wanda shi ma ya tafka asara mai yawa cewa ya yi:  “Ban dade da saro kaya ba  daga kantin SPAAR na zuba a shagon ga shi duk sun kone babu abin da ya tsira  kuma na sayo janareto da talabijin din bango fankoki da kwamfutoci na zuba a shagon ga shi  duk gobarar ta lashe su. Ni ina burin cin kasuwar kirsimeti”.inji shi.

Wakilinmu ya yi ta bakin kokarinsa domin jin ta bakin shugabannin kasuwar watt, amma al’amarin  ya ci tura. Domin gano musabbabin gobarar da kuma kiyasin asarar dukiyar da aka yi, amma ya zuwa rubuta labarin an ce sun shiga dakin taro.