Gobara ta lakume dukiya da rai daya a Kalaba
An tafka asarar kadararori da rai daya a wata gobara da ta tashi, ranar Litinin din da ta gabata a wani kamfanin adana danyen man fetur a Kalaba, ranar da ke wani kamfani mai suna Dozzi a Kalaba, Jihar Kuros Riba, kamar yadda wani mutum da al’amarin ya auku a gabansa, Alhaji Ahmad Alfa Yahaya […]
An tafka asarar kadararori da rai daya a wata gobara da ta tashi, ranar Litinin din da ta gabata a wani kamfanin adana danyen man fetur a Kalaba, ranar da ke wani kamfani mai suna Dozzi a Kalaba, Jihar Kuros Riba, kamar yadda wani mutum da al’amarin ya auku a gabansa, Alhaji Ahmad Alfa Yahaya ya shaida wa Aminiya.
Ya ce musabbabin gobarar shi ne ana kokarin dura wa wata motar tanki da ke dakon man fetur zuwa sassan kasuwanni, domin raba wa masu saye, ana cikin haka tankin man fetur din yaron mota yana korarin rike bakin bututun da ke dura mai yayin da shi kuma direba yana sama, yana lura da tafiyar na’urar da ke dura masa man, domin ya tabbatar da hakikanin ko lita nawa na garwar man fetur zai dauka ne.
“Sai wani karfe ya fado daga saman mota, faduwarsa ke da wuya, sai ya fada kan wani karfe kasan fetur da wuta karfen, sai ya yi tartsatsi kan wata waya, sai wuta ta tashi fa, daga nan ne fa sai hayaki ya turnuke wuta ta kama,” inji shi.
Alhaji Alfa Yahaya ya ce a wannan hadari, mutum daya ne ya mutu, babu wadanda suka samu rauni, sakamakon namijin kokarin da jami’an kashe gobara suka yi da kuma dauki da jama’a suka rika bayarwa na kawar da motoci, kada gobarar ta watsu. A kalla dukiya ta sama da Naira milyan 10 ce aka tafka asararta.