Gobara ta lakume dukiya da shaguna 300 a karar shanu ta Isheri
dakunan kwana da Shagunan kasuwanci fiye da 300 na katako suka kone kurmus a wata gobara da ta tashi a cikin babbar kasuwar Karar shanu ta Isheri a Jihar Ogun. Sai dai babu wanda ya rasa ransa a gobarar da ta tashi da misalin karfe takwas na daren ranar Lahadi da makon jiya.Da yake yi […]
dakunan kwana da Shagunan kasuwanci fiye da 300 na katako suka kone kurmus a wata gobara da ta tashi a cikin babbar kasuwar Karar shanu ta Isheri a Jihar Ogun. Sai dai babu wanda ya rasa ransa a gobarar da ta tashi da misalin karfe takwas na daren ranar Lahadi da makon jiya.
Da yake yi wa Aminiya bayani Sarkin Hausawan Isheri, wanda yake jagorantar kasuwar ta Kara, Isheri, Alhaji Badamasi Mu’azu, ya ce, “da misalin karfe bakwai da rabi zuwa takwas na daren ranar Lahadi ne wuta ta fara tashi daga wani sashe na mazauna wannan kasuwa da suka yi iya kokarinsu, tare da hadin gwiwar mutane daga wajen kasuwar suka shawo. Kasancewar mafi yawancin dakuna da shaguna da ke cikin kasuwar ginin katako ne, shi yasa ba a iya kashe wutar cikin kankanen lokaci ba. Ma’aikatan kashe gobara sun bayyana a wannan wuri ba tare da wadataccen ruwa da isassun kayan aiki ba. Jama’a ne suka taimaka aka kashe wannan wuta da aka yi sa’o’i biyar tana ci. Muna godiya ga Allah (SWT) da yasa gobarar ta tsaya a kan wadannan dakuna da shaguna, ba tare da an rasa rayukan mutane da dabbobi ba.”
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen wannan kasuwa Alhaji Ahmadu Usman, ya ce, “har zuwa yanzu muna yin bincike, domin gano musabbabin wannan gobara wacce ta lakume dukiyar jama’a ta miliyoyin Naira. Dole ne a samu cunkoso a yanzu da masu fataucin dabbobi daga Arewacin kasa suke rububin shigowa cikin wannan kasuwa, domin sayar da ragunan salla ga mabukata. Amma dai Alhamdulillahi da ba a samu mutuwar mutane ko dabbobi a dalilin wannan gobara ba.”