Gobara ta lakume kasuwar ’yan Katako a Kaduna
Wata gobara ta kone kasuwar ’yan katako da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna. Binciken Aminiya ya gano cewa gobarar ta tashi ne cikin dare da misalin karfe 4 a ranar Juma’a. Gobarar ta yi sanadin kone kayan katako na miliyoyin Naira. Mutanen yankin da suka kai dauki don kashe wutar ba su […]
Wata gobara ta kone kasuwar ’yan katako da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.
Binciken Aminiya ya gano cewa gobarar ta tashi ne cikin dare da misalin karfe 4 a ranar Juma’a.
Gobarar ta yi sanadin kone kayan katako na miliyoyin Naira.
Mutanen yankin da suka kai dauki don kashe wutar ba su yi nasara ba, lamarin da ya sa dole sai da ’yan kwana-kwanar jihar suka kawo musu dauki.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban ’Yan Kasuwar Katakon Sabon Gari, Suleiman Yusuf-na-Hari, ya ce wannan ita ce gobara mafi muni da kasuwar ta taba fuskanta a tarihi.
Sai dai ya ce har yanzu ba a gano musabbabin tashin wutar ba.
A cewarsa mutanen da ke kusa da kasuwar da wasu daga cikin masu gadinta sun gaza kashe wutar sai da taimakon Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, inda ta kai su har karfe 10 na safe gabanin su shawo kanta.
Alhaji Suleiman ya jajanta wa wadanda iftila’in gobarar ya shafa yana mai kira da su dauki hakan a matsayin kaddara.
Kazalika, ya roki Gwamnatin Jihar da ta Tarayya kan su taimaka wa ’yan kasuwar da gobarar ta shafa.