Gobara ta lakume muhimman takardu a Sakatariyar Jama’a

Mahukunta a Karamar Hukumar Jama’a da ke jihar Kaduna a yau Litinin sun ce, gobarar da ta auku a ofisoshi uku na Sakatariyar Karamar hukumar ta yi sanadiyyar asarar muhimman takardu da sauran abubuwa ofis. Shugaban Karamar Hukumar Mista Peter Averik, ne ya sanar da hakan a ofishinsa da ke Kafanchan. Ya ce, jami’an tsaro […]

Gobara ta lakume muhimman takardu a Sakatariyar Jama’a

Mahukunta a Karamar Hukumar Jama’a da ke jihar Kaduna a yau Litinin sun ce, gobarar da ta auku a ofisoshi uku na Sakatariyar Karamar hukumar ta yi sanadiyyar asarar muhimman takardu da sauran abubuwa ofis.

Shugaban Karamar Hukumar Mista Peter Averik, ne ya sanar da hakan a ofishinsa da ke Kafanchan. Ya ce, jami’an tsaro na sakatariyar ne suka fara sanar da tashin gobarar da misalin 2:15 na tsakar dare. Daga nan aka sanarwa jami’an hukumar kashe gobara inda suka yi nasarar kashe gobarar.