Gobara ta lakume sama da shaguna 200 a kasuwar Benuwe

Sama da shaguna 200 ne gobara ta lakume a kasuwar zamani da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe a yammacin jiya Talata. Tashin gobarar ta fara ne da misali karfe 6:30 na yamma a tsakiyar kasuwar bayan lokacin da duk ‘yan kasuwar suka rufe shagunansu suka koma gida. Ba a samu rahoton asarar rayuka ba, […]

Gobara ta lakume sama da shaguna 200 a kasuwar Benuwe

Sama da shaguna 200 ne gobara ta lakume a kasuwar zamani da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe a yammacin jiya Talata.

Tashin gobarar ta fara ne da misali karfe 6:30 na yamma a tsakiyar kasuwar bayan lokacin da duk ‘yan kasuwar suka rufe shagunansu suka koma gida.

Ba a samu rahoton asarar rayuka ba, sai dai an a kalla shagunan da ke rufe 100 ne gobarar ta lakume da sauran rumfunan kasuwar. An samu asarar biliyoyin Naira sanadiyyar tashin gobarar.