Gobara ta lakume shaguna 14 a Kasuwar Jos
An samu tashin gobara a kasuwar Katako da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato inda ta cinye shaguna 14. Wakilinmu da ya ziyarci kasuwar ya ce gobarar ta cinye duk shagunan da yankin gobarar ta kama. Shugaban Body B Lawal Kamal, ya tabbatarwa da wakilinmu cewa, gobarar ta fara tashi ne da […]
Gobarar da ta kama a kasuwar Jos
An samu tashin gobara a kasuwar Katako da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato inda ta cinye shaguna 14.
Wakilinmu da ya ziyarci kasuwar ya ce gobarar ta cinye duk shagunan da yankin gobarar ta kama.
Shugaban Body B Lawal Kamal, ya tabbatarwa da wakilinmu cewa, gobarar ta fara tashi ne da misalign karfe 3:30 na tsakar daren yau, kafin zuwan jami’an kashe gobara shagunan sun kone kurmus. Sannan ana kyautata zaton gobarar ta tashi ne sanadiyyar wutar lantarki.