Gobara ta lakume shaguna a kasuwar Anambra

An samu mummunan gobara a kasuwar sayar da karafunan motoci da sauran kayayyakin mota da ke Awada a Onitsha jihar Anambra. Wutar ta tashi ne da misalin karfe 1:30 na tsakar daren yau Asabar. Sai dai ba a sanar da asarar rai ba zuwa yanzu sakamakon tashin gobarar, saboda babu kowa a cikin rumfunan da […]

Gobara ta lakume shaguna a kasuwar Anambra

An samu mummunan gobara a kasuwar sayar da karafunan motoci da sauran kayayyakin mota da ke Awada a Onitsha jihar Anambra.

Wutar ta tashi ne da misalin karfe 1:30 na tsakar daren yau Asabar.

Sai dai ba a sanar da asarar rai ba zuwa yanzu sakamakon tashin gobarar, saboda babu kowa a cikin rumfunan da gobarar ta tashi.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Anambra SP Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwar gobarar.