Gobara ta lakume uwa da ’yarta a Kalaba
Wata gobara da ta tashi a sakamakon zuba wa injin janareto mai ta lakume rayukan uwa da ’yarta a unguwar da ake kira Mil 8 da ke garin Kalaba, yankin karamar Hukumar Kalaba, Jihar Kurosriba, a makon jiya. Wani wanda gobarar ta tashi kusa da shi, wanda har wa yau makwabcin mamatan ne, mai suna […]
Wata gobara da ta tashi a sakamakon zuba wa injin janareto mai ta lakume rayukan uwa da ’yarta a unguwar da ake kira Mil 8 da ke garin Kalaba, yankin karamar Hukumar Kalaba, Jihar Kurosriba, a makon jiya.
Wani wanda gobarar ta tashi kusa da shi, wanda har wa yau makwabcin mamatan ne, mai suna Ime Ekpeowo, ya shaida wa Aminiya cewa matar gidan ce da kanta ta zo da fitilar kwai tana dura wa tankin janareton man fetur, daga nan kuwa sai wuta ta tashi ta watsu zuwa sauran sassan gidan, har ma da na makwabta.
Makwabcin ya ci gaba da cewa, da kyar ya tsira, shi da matarsa. “Ita ma kanta mamaciyar, tare da ita aka fara gudun tsira, sai ta tuna ai ta bar ’yarta a cikin daki; don haka ta koma ta dauko ta. Daga nan ne fa aka yi biyu babu,” inji shi.
Duk iyaka kokarin da jami’an kashe gobara suka don kashe wutar, sai da gobarar ta yi ta’adin gaske, inda ta kone gidan da kadarorin da ke cikinsa gaba daya.
Da ya kai ziyarar ganin irin barnar da gobarar ta yi wa gidan, shugaban hukumar bayar da agajin gaugawa na Jihar Kurosriba, Sema bincent Akuoh, ya gargadi mutane da su rika yin hattara, yayin da duk suka zo zuba wa janaretonsu man fetur; su gu ji zuwa da wuta ko wata fitila da haskenta ka iya sanyawa fetur ya kama da wuta.