Gobara ta lalata buhun albasa sama da 5,800 a Sakkwato

Ƙungiyar manoman ta roƙi gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wa waɗanda gobarar ta shafa.

Gobara ta lalata buhun albasa sama da 5,800 a Sakkwato

Wata gobara da ta tashi ta lalata buhun albasa 5,832 a ƙauyen Duhuwa da ke Jihar Sakkwato, lamarin da ya jawo manoma asara mai tarin yawa.

Wannan shi ne karo na uku cikin mako guda da irin wannan gobara ta auku a wuraren ajiyar albasa a jihar.

Gobarar ta faru ne a ranar Juma’a inda ta ƙone rumbunan ajiyar albasa guda 324, kuma kowanne rumbu na ɗauke da buhu 18 na albasa.

Shugaban Ƙungiyar Manoma, Sarrafawa da Kasuwancin Albasa ta Ƙasa (NOPPMAN), Aliyu Maitasamu Isah, ya ce an yi asara ta kimanin Naira miliyan 204, bisa farashin buhu ɗaya na albasa da ake sayarwa kan Naira 35,000 a ƙauyen.

Mazauna yankin sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 2 na rana kuma ta ci gaba da ci har zuwa ƙarfe 5 na yamma.

Ta bazu cikin sauri zuwa rumbunan ajiyar albasa tare da shafar wani gida da ke kusa da su.

A makon da ya gabata ma, wata gobara a ƙauyen Kojiyo ta lalata buhun albasa 2,275 da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 56.8.

Haka kuma, wata gobara da ta tashi a ƙauyen Dundaye, inda sama da buhu 2,000 suka lalace.

Ɗaya daga cikin manoman da abin ya shafa, Bashiru Muhammadu, wanda ya rasa buhu 260, ya bayyana lamarin a matsayin babban tashin hankali.

“Wannan shi ne abincinmu da kuma hanyar samun kuɗinmu. Yanzu mun rasa komai,” in ji shi.

Wani manomi, Muddaha Yusuf, ya ce rashin samun ruwa a kusa ya sa gobarar ta yi muni sosai domin ba a samu damar kashe ta da wuri ba.

Sarkin ƙauyen Duhuwa, Magaji Salihu, ya ce sama da rumbuna 300 ne suka ƙone, sannan ya roƙi gwamnati da masu hannu da shuni su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

NOPPMAN ta ce yawaitar irin waɗannan gobara abun ban tsoro, kuma sun kai rahoto ga ’yan sanda da DSS domin yin bincike.

Ƙungiyar ta kuma roƙi gwamnatin Jihar Sakkwato, NEMA da SEMA da su tallafa wa manoman, sannan ta ce an yi asarar sama da Naira miliyan 500 a dukkanin gobarar uku da aka yi a yankin.