Gobara ta lalata kayan miliyoyin Naira a coci
Gobarar wadda ta tashi da tsakar dare da ba a san takamaiman silarta ba ta ƙone abubuwa ƙurmus, tare da lalata dukiyoyi.
Wata gobarar da ta tashi a cocin Cherubim and Seraphim mai suna Irapada Kristi, da ke kan Titin Eleye a birnin Akure na Jihar Ondo, ta lalata dukiyoyin da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.
Gobarar wadda ta tashi da tsakar dare da ba a san takamaiman silarta ba ta ƙone abubuwa ƙurmus, tare da lalata dukiyoyi.
Shaidu sun shaida wa manema labarai cewa, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar dare a ranar Laraba, inda aka ce ta somo ne daga tsakiyar cocin kafin ta mamaye ko’ina ta kuma ƙone gaba ɗaya gini.
Mutanen da ke zaune a yankin sun yi cincirindo zuwa wajen domin ƙoƙarin kashe gobarar ta hanyar amfani da kwanukan ruwa, amma ƙoƙarin nasu bai nasara ba sakamakon yadda wutar ta riga ta ci ƙarfi.
“Mutanen da ke zaune a yankin sun fito suna zuba ruwa daga kwanuka domin kashe wutar, amma ƙoƙarin bai yi amfani ba, saboda wutar ta riga ta fi ƙarfin kowa,” in ji ɗaya daga cikin shaidun.
An yi Ƙoƙarin tuntuɓar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Ondo domin kawo ɗauki bai nasara ba.
To sai dai kuma, yayin da take magana da jaridar Daily Trust, shugabar cocin da aka fi sani da ‘Iya Ewe’, ta bayyana cewa har yanzu ba ta gama tantance abin da ya haifar da gobarar ba.
A cewarta, ta bar cocin ne tun daren Ranar Lahadi ba tare da ta bar wata wuta a kunne ba, sannan ta yi watsi da yiwuwar cewa matsalar lantarki ce ta haifar da gobarar, inda ta bayyana cewa tsarin lantarkin ginin ya shafe shekaru yana aiki ba tare da wata matsala ba.
Ta nuna alhinin cewa gobarar ta haifar da babbar lalacewa ga cocin tare da ƙone kayayyaki masu darajar miliyoyin naira.
Babu wanda ya rasa ransa kuma babu wanda ya ji rauni a lamarin.