Gobara ta tashi a fadar Sarkin Daura

Rahotanni sun ce ko tsinke ba a dauka ba bangaren da gobarar ta cinye

Gobara ta tashi a fadar Sarkin Daura

Gobara a fadar Sarki Daura

Kayayyaki na miliyoyin Naira sun kone bayan wata gobara ta tashi a fadar Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq Umar.

Rahotanni sun ce wutar ta tashi ne wajen misalin karfe 4:00 na yammacin Litinin kuma ta shafe sa’o’i tana ci, sai da cinye kusan komai a bangaren da dan Sarkin, kuma Danburan na Daura yake.

Basaraken dai, Alhaji Muhammadu Daha Umar Farouq Umar, shi ne Hakimin Baure.

Rahotanni sun ce ba a sami asarar rai ba, saboda matar basaraken, wacce ’ya ce ga marigayi Sarkin Daura, Muhammadu Bashar, ta yi tafiya lokacin da lamarin ya faru.

Majiyoyi sun ce, “Ko tsinke ba a dauka ba a sashen da gobarar ta tashi, amma dai ba a sami asarar rai ba.

“Muhimman abubuwa da dama ne suka kone ciki har da muhimman takardu,” in ji majiyar.

Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin masarautar, Sarkin Labaru Usman Yaro ya ce kodayake ba a kai ga tantance musabbabin gobarar ba, amma ba za ta rasa nasaba da wutar lantarki ba.

Sai dai ya gode wa jami’an kashe gobara da ma jama’ar ta Daura da suka taimaka waen kashe wutar.

’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo

Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano

Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad

Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC