Gobara ta tashi a gidan gwamnatin SakAkwato

A ranar Talatar da ta gabata ce da misalin karfe uku rana, wata gobara ta tashi a tankar mai da ke dauke da fetur, wacce ke aje cikin gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato. Gobarar ta yi nasarar lashe wasu ababubuwan hawa, kafin a samu nasarar kashe ta. Imam Imam shi ne mai magana da yawun Gwamna […]

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin SakAkwato
Gobara ta tashi a gidan gwamnatin SakAkwato

A ranar Talatar da ta gabata ce da misalin karfe uku rana, wata gobara ta tashi a tankar mai da ke dauke da fetur, wacce ke aje cikin gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato. Gobarar ta yi nasarar lashe wasu ababubuwan hawa, kafin a samu nasarar kashe ta.

Imam Imam shi ne mai magana da yawun Gwamna Tambuwal, ya kara wa manema labarai bayani kan gobarar. “Babbar mota ce ta daukar mai da ta lalace, ta yi sanadiyar wannan wutar; domin ita ce ta kama. A dan lokaci kadan da tashin wutar, jami’an kashe wuta na jiha da masu sayar da ruwa suka yi kwamba suka tunkari wutar. Ba su nuna wata gajiyawa ba har suka samu nasarar kashe ta” Inji shi.
Ya wara da cewa, babu hasarar rayuwa ko wani mummunan rauni kuma dukkan kayan gwamnati ba wanda aka yi asararsa
Mataimakin Gwamna, Alhaji Ahmad Aliyu da Kwamishinan ’yan sanda, Abdullahi Fagge da Sakataren Gwamnatin jiha, Farfesa Bashir Garba da Kwamishinan cikin gida, Alhaji Isah Sadik Acida; duk sun ziyarci wajen, inda shi mataimakin na gwamna ya umarci jami’an na kwana-kwana da su tsaya wurin don gudun sake tashin wutar, kuma ya gode wa mutane saboda irin sadukarwa da suka nuna.