Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja

Mutane sun tsere daga wajen domin tsira da rayukansu.

Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja

Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba.

Shaidu sun ce gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man fetur, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba kasancewar sauran tankunan mai maƙare suke da fetur.

Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen don shawo kan lamarin, amma har yanzu wutar na ci gaba da yaɗuwa.

“Babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa, amma mutane sun tsere domin tsira da rayukansu,” in ji wani mutum, mai suna Abba Mohammed.

Ƙoƙarin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa