Gobara ta tashi a gidan Shah Rukh Khan
A kwanakin baya ne wata gobara ta tashi a gidan Shah Rukh Khan, wanda ke yankin Wadala da Nariman.Kamar yadda rahoto ya bayyana, wutar dai ta tashi a gidan da daren Alhamis, a sakamakon tangardar wutar lantarki da aka samu.Kamar yadda bincike ya tabbatar, bayan da wutar ta taso daga wani dakin wanka da ke […]

A kwanakin baya ne wata gobara ta tashi a gidan Shah Rukh Khan, wanda ke yankin Wadala da Nariman.
Kamar yadda rahoto ya bayyana, wutar dai ta tashi a gidan da daren Alhamis, a sakamakon tangardar wutar lantarki da aka samu.
Kamar yadda bincike ya tabbatar, bayan da wutar ta taso daga wani dakin wanka da ke gidan, sai na’urar da ke bayyana alamar hadari ta kashe kanta. Nan da nan sai masu gadi suka sanar da ’yan kwana-kwana, wadanda cikin kankanen lokaci suka kawo motocin kashe goabara guda biyu zuwa gidan.
An samu bayani daga masu gadin gidan, cewa gobarar ba ta ta’azara ba, wanda dalili ke nan cikin lokaci kankane suka samu damar kashe ta.
Jim kadan da faruwar wannan gobara, sai dan wasa Shah Rukh Khan ya yi bayani a turakarsa ta Twitter, inda ya ce: “Ya zuwa yanzu dai an gama kashe wutar kuma ba a samu wata asara ba. Ina godiya ga dukkan ma’aikatan da suka taka rawa wajen wannan aiki.”
Shah ya karkare batunsa na Twitter da raha, inda ya ce: “Yanzu dai tunda wuta ta kama gidana, sai ku zo mu ji dumi ko? Kodayake fa haka bai dace ba!”