Gobara ta tashi a gini mai hawa 17 a Legas

Lamarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 11:33 na safe ranar Alhamis, ya shafi wata mota ce ƙirar saloon a ginin mai hawa 17.

Gobara ta tashi a gini mai hawa 17 a Legas

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas ta yi nasarar kashe wata gobara da ta tashi a hawa na uku na ginin bankin Polaris da ke kan titin Broad Street a yankin Lagos Island.

Lamarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 11:33 na safe ranar Alhamis, ya shafi wata mota ce ƙirar saloon da ke ajiye a hawa na uku na ginin mai hawa 17, wanda kuma ake amfani da shi azaman wurin ajiye motoci.

A cikin wata sanarwa da Babban Jami’ar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Margaret Adeseye ta fitar, ta bayyana cewa an tura jami’an kashe gobara daga rassan Ebute Elefun da Sari Iganmu zuwa wurin da abin ya faru nan take bayan samun kiran gaggawa.

“Hukumar Kashe Gobara  ta Jihar Legas ta yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a hawa na 3 na ginin bankin Polaris, mai lamba 61/65 Broad Street, a Lagos Island.

Abin da ya lalace kawai shi ne motar da gobarar ta shafa da kuma  rukunin da ke kusa da ita. Ba a sami rahoton asarar rai ko raunuka ba,” in ji ta.

Hukumomi ba su bayyana musababin tashin gobarar ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Majiyar PUNCH Online ta rawaito cewa, bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna  hayaƙi na tashi daga ginin, yayin da mazauna unguwar da ’yan kasuwa suka taru a kewayen wurin da lamarin ya faru.