Gobara ta tashi a ginin Babban Bankin Najeriya a Ikko

Ginin babban bankin Najeriya a Ikko ya kama da wuta a ranar Talata  da misalin karfe 6 na maraice daga hawan da ofishin gwamnan baban bankin yake, sai dai lokacin da wakilin Aminiya ya isa wurin da misalin karfe 8 har an riga an kashe wutar.Sai dai kuma ba wani cikakken bayanin musabbabin wutar yayin […]

Gobara ta tashi a ginin Babban Bankin Najeriya a Ikko
Gobara ta tashi a ginin Babban Bankin Najeriya a Ikko

Ginin babban bankin Najeriya a Ikko ya kama da wuta a ranar Talata  da misalin karfe 6 na maraice daga hawan da ofishin gwamnan baban bankin yake, sai dai lokacin da wakilin Aminiya ya isa wurin da misalin karfe 8 har an riga an kashe wutar.
Sai dai kuma ba wani cikakken bayanin musabbabin wutar yayin da wasu ke cewa  na’urori  ne da aka bari kunne, wasu suna cewa mai yiwuwa akwai wata makarkashiya da aka kulla.
Wakilin Aminiya ya iske wajen na cike da jami’an tsaro. Yayin da ya nemi sanin ko akwai mutane cikin ginin sa’ilin da gobarar ta faru, wasu sun shaida masa cewa mutanen da ke ciki ba su da yawa, sai dai an ce har an fito da wani mutum, wanda aka wuce da shi zuwa asibiti, amma ba wanda ya san ko wane irin lahani gobarar ta yi masa.
Da yake har sa’ilin rubuta wannan labarin ba a samu dalilin wannan gobara ba, amma  masana  harkokin kudi,  musamman  abin da ya shafi  harkokin banki,  suna  alakanta lamarin ne da batutuwan  sayar da  bankin Intercontinental da kuma bankin Access. Sai kuma batun bankin masana’antu, wanda aka ce shugabar bankin ta biya kudi  masu tarin yawa ga babban bankin kuma duk takardun  wannan kasuwancin yana wannan hawan da ya kone ne.
Wani jami’i da bai yarda a ambaci sunansa ba ya ce hukumar bankin za ta samar  da  kwamiti  mai karfin gaske domin binciken wannan lamari  kuma  ya ce  ya fi  ba da karfinsa  ga cewa  akwai  zagon kasa  cikin wannan lamarin domin a hawan da abin ya faru, akwai muhimman takardu  da kusan ya shafi harkokin kasuwanci ko kuma kudi tsakanin babban bankin da sauran bankinan kasa.