Kano Poly ta yi Gobara

Gobarar ta kone daukacin sashen al’adu da masana’antu na kwalejin.

Kano Poly ta yi Gobara

‘Yan kwana-kwana na kashe gobarar Bangledash

Gobara ta tashi a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kano (Kano Poly) a safiyar  ranar talata.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta sanar cewa gobarar ta kone daukacin sashen al’adu da masana’antu na kwalejin.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce kawo yanzu ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ko girman barnar da ta yi ba.

Saminu Abdullahi ya kara da cewa mhaukunta na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin domin gano hakikanin abin da ya faru.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda