Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano

An tafka asarar dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a sanadiyyar gobarar ta safiyar Litinin, yayin da ake ci gaba da aiki ceto

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke Kano

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke birnin Kano a safiyar Litinin ɗin nan.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwa da mazauna sun shiga tashin hankali matuƙa sakamakon tashin gobarar a shahararriyar kasuwar kayan abincin kwali da da ke titin Bello Road.

‎An yi asarar dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a sanadiyyar gobarar ta safiyar Litinin, yayin da ake ci gaba da aiki ceto.

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano musabbin gobarar ko girman ɓarnar da ta yi ba.