Gobara ta tashi a babbar cibiyar samar da lantar a Kebbi

Gobara ta tashi da tsakar dare a ofishin Kamfanin Samar da Wutar Lantarnki na Najeriya (TCN) da ke Birnin Kebbi.

Gobara ta tashi a babbar cibiyar samar da lantar a Kebbi

Gobara ta tashi da tsakar dare a ofishin Kamfanin Samar da Wutar Lantarnki na Najeriya (TCN) da ke Jihar Kebbi.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12.30 da dare, kuma zuwa lokacin da wakilinmu ya turo rahoto ba a kai ga gano musabbabinta ba.

Mazauna yankin Mechanic Village inda ofishin yake a garin Birnin Kebbi, sun shaida wa wakilinmu cewa da farko sun ji karar fashewar wani abu ne sannan hayaki ya turnuke, kafin daga baya wuta ta tashi daga wurin.

Hakan kuwa ya faru ne sa’o’i kadan daukewar wutar lantarki a fadin Najeriya a sakamakon durkushewar babban layin lantarki na TCN.

An dauke wutar a fadin Najeriya ne makonni kadan bayan TCN ta yi bikin cika shekara guda ba tare da daukewar wuta gaba daya a layin ba. Daga bisani dai an dawo da wutar.

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ta ce an dauke wutar ne a sakamakon gobarar da ta tashi a layin lantarki mai karfin 330kV da ke Kainji/Jebba wanda ya yi sanadin daukewar rasa Megawatta 356.63 na karfin wutar lantarki.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna