Gobara ta tilasta wa mutum dubu biyar barin gidajensu

Kimanin mutum dubu biyar ne suka rasa matsugunansu bayan da gobara ta kone dakunan kwanansu a wata unguwa ta ’yan-share-wuri-zauna a yankin Ebute Meta da ke Jihar Legas.Binciken Aminiya ya gano cewa gobarar ta tashi ne a cikin makon da ya gabata da misalin karfe  biyu na dare inda ta yi kimanin awanni uku tana […]

Gobara ta tilasta wa mutum dubu biyar barin gidajensu

Wani sashe na inda gobarar ta koneKimanin mutum dubu biyar ne suka rasa matsugunansu bayan da gobara ta kone dakunan kwanansu a wata unguwa ta ’yan-share-wuri-zauna a yankin Ebute Meta da ke Jihar Legas.
Binciken Aminiya ya gano cewa gobarar ta tashi ne a cikin makon da ya gabata da misalin karfe  biyu na dare inda ta yi kimanin awanni uku tana ci. Wadanda lamarin ya shafa sun bayyana cewa ba su san musabbabin tashin wutar ba, amma sun ce suna zargin gobarar ta auku ne sakamakon kyandir da wasu mazauna wurin suka kunna saboda rashin wutar lantarki. Amma an gano cewa abu-buwan da mazauna wurin suka yi amfani da su wajen gina gidajen nasu ya karawa wutar karfi.
Mazauna wurin da suka shafe shekaru da dama a wurin, sun bayyana cewa ba su da wurin da za su je saboda dadewar da suka yi a wurin. Sun bayyana cewa wutar ta kone dukkan abubuwan da suka mallaka, amma sun bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa a gobarar.
Mazaunan sun bayyana cewa gobarar ita ce karo na uku da take tashi a wurin sakamakon halin ko-in-kula na mazauna wurin. daya daga cikin shugabannin unguwar Ifesowapo mai suna Ishola Agbodemu ya bayyana cewa gobarar ta yi musu barna sosai. Ya zargi gwamnatin jihar da yin watsi da su ba tare da sama musu gidaje ba duk da harajin da suke biyan gwamnati.
Ya ce, “Babu wanda yake fatan ya zauna a irin wannan wuri, amma saboda ba mu da gwamnati mai kyau a wannan kasa, mutane fiye da dubu bakwai suna zaune a wannan wuri, amma duk da haka gwamnati ta ki ta  samar wa da talakawa gidaje. Mun gina gidajenmu da kanmu da katako da kwanuka kuma a wannan wuri na fi shekaru 25, ba bin da gwamnati take yi mana sai tashinmu karfi da yaji, ba mu samu kwanciyar hankali ba, sai da babbar kotu da ke unguwar Igbosere ta dakatar da gwamnati daga tashinmu”.