Gobara ta varnata dukiya da dabbobi masu yawa a Jigawa
Kimanin dabobi 30 ne da gidaje sama da 25 suka qone qurmus a qauyan Abanderi da ke Qaramar Hukumar Dutse, sakamakon wata gobara da ta tashi a ranar Lahadin da ta gabata da misalin qarfe 12.30 na rana. Gobarar da ta yi tsawon awa huxu tanaci, an kasa shawo kanta har sai da jami’an kashe […]
Kimanin dabobi 30 ne da gidaje sama da 25 suka qone qurmus a qauyan Abanderi da ke Qaramar Hukumar Dutse, sakamakon wata gobara da ta tashi a ranar Lahadin da ta gabata da misalin qarfe 12.30 na rana.
Gobarar da ta yi tsawon awa huxu tanaci, an kasa shawo kanta har sai da jami’an kashe gobara suka kawo xauki.
Da yake jawabi, muqaddashin Darakta na Hukumar Kashe gobara ta Jihar Jigawa, Alhaji Bashir Tijjani Abubakar ya ce gobarar ta tashi ne tun da misalin qarfe 1230 na rana, inda dabbobi sama da talatin da kayan abinci da kuma gidaje sama da 25 suka qone a lokacin da wutar ta faru.
Ya qara da cewa har zuwa lokacin da muke zantawa da shi, hukumarsu ba ta sami sahihin abin da ya haddasa wutar ba amma dai sun sami jita-jitar cewa wasu matasa ne suke gasa zabuwa a bayan gari, shi ne wutar ta fi qarfinsu ta faxa cikin gari, yayin da wata majiya ta shaida masu cewa wasu ne suke qone yayi a gona, daga can ne wutar ta tashi, ta afka cikin gari.
Ya nuna takaicinsa na rashin sanar da su a kan lokaci, inda ya ce hakan ya faru ne sakamakon ba kowane yake da lambobin wayarsu ba amma yanzu za su samar da lambobin wayoyinsu a dukkan alluna a cikin gari domin hakan zai taimaka wajen sanar da hukumar idan buqatar hakan ta taso.