Gobara ta yi ajalin ɗalibai 17 a makarantar firamare a Kenya
Gobara a makarantu ba sabon al’amari ba ne a makarantun kwana a Kenya
Gobarar da ta tashi a ɗakunan kwanan ɗalibai a wata makarantar firamare a Kenya ta kashe ɗalibai 17 tare da jikkata 13.
Kakakin rundunar ’yan sandan ƙasar, Resila Onyango ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP a ranar Juma’a cewa gawarwakin da aka gano sun ƙone sosai “ta yadda ba za a iya gane su ba.
- Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa fursunoni kashi 50 a kuɗin abinci
- Ambaliya ta kashe mutane 20 da gidaje a Yobe
“An soma gudanar da bincika game da gobarar da ta tashi a makarantar firamare ta Hillside Endarasha da ke yankin Nyeri, a cewar Resila Onyango.
“Akwai yiwuwar sake gano ƙarin gawarwaki idan masu aikin ceto suka tsananta aikinsu a wurin” in ji ta.
Shugaban ƙasar, William Ruto ya kira gobarar da “mummunar gobara mai tayar da hankali” sanan ya buƙaci gudanar da bincike game da lamarin.
“Na bayar da umarni ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike game da wannan mummunan lamari.
“Duk wanda aka samu da sakacin da ya haddasa gobarar zai fuskanci hukunci,” a cewar shugaba William Ruto a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.
Ƙungiyar bayar da agaji ta Kenya Red Cross ta wallafa saƙo a shafin X da ke cewa tuni hukumomi suka rufe makarantar.
A shekarun baya bayan nan, Gobara a makarantu ba sabon al’amari ba ne a makarantun kwana a Kenya, inda da yawa daga cikinsu ake zargin ana tashinsu ne da gangan.
Ɗalibai aƙalla 10 suka mutu a gobarar da ta tashi a wata makarantar sakandiren mata ta Moi da ke Nairobi a watan Satumba na 2017, wadda gwamnati ta ce da gangan aka tashe ta.
A shekarar 2001, ɗalibai 58 sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi da ɗakunan kwanansu a makarantar Sakandare ta Kyanguli da ke wajen birnin Nairobi.
Kazalika a shekarar 2012, ɗalibai sun mutu a makarantar Homa Bay County da ke yammacin Kenya.
Haka ma a shekarar 2014 aƙalla ɗalibai 67 ne suka mutu a gundumar Machakos da ke kudu maso gabashin birnin Nairobi, sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wata makaranta.