Gobara ta yi ajalin magidanci da iyalansa hudu a Suleja

Wani magidanci da ke sana’ar dillancin gida da fulotai a garin Suleja ta Jihar Neja mai suna Malam Ibrahim Maiwada ya gamu da ajalinsa tare da iyalansa hudu a ranar Alhamis din makon jiya bayan da gobara ta mamaye gidan da yake ciki da misalin karfe 11:00 na dare lokacin da suke barci.  Lamarin wanda […]

Gobara ta yi ajalin magidanci da iyalansa hudu a Suleja
Gobara ta yi ajalin magidanci da iyalansa hudu a Suleja

Wani magidanci da ke sana’ar dillancin gida da fulotai a garin Suleja ta Jihar Neja mai suna Malam Ibrahim Maiwada ya gamu da ajalinsa tare da iyalansa hudu a ranar Alhamis din makon jiya bayan da gobara ta mamaye gidan da yake ciki da misalin karfe 11:00 na dare lokacin da suke barci. 

Lamarin wanda ya faru a yankin Checheniya a garin na Suleja, ana zargi ya biyo bayan dawo da wutar lantarki mai karfi ne a yankin, kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Iyalansa hudu da suka rasu, sun hada da uwargidansa mai suna Saratu Ibrahim da ’ya’yansa uku da suka hada da A’isha mai shekara 6 da Fatima mai shekara 3, sai kuma Muhammad mai wata hudu.
Sai dai amaryarsa da ya aura kasa da wata shida da ’yarsa karama da kuma wani kanensa, sun kubuta da rai daga gobarar, bayan jama’ar da suka kawo dauki sun fasa tagar falon gidan inda suka same su a ciki.
Malam Ibrahim Isa, wanda marigayin ke haya a wajensa ya bayyana wa wakilimu cewa, gidan wanda ke da bangarori biyu, marigayin na haya a cikin guda a yayin da shi kuma ke zaune a gida na biyu, ya ce ya ankara da al’amarin ne a lokacin da ya ji hayaniyar jama’a da suke taimakawa a yayin gobarar. A lokacin ne inji shi ya tayar da matansa biyu da ’ya’yansa suka fice daga bangarensu cikin hanzari.
Ya ce daga nan ne kuma sai ya koma bangaren marigayin inda ya samu jama’a sun kubutar da mutum uku da daga falon gidan. Ya ce “Bayan na shaida masu cewa mutanen da ke cikin gidan sun zarce uku, mun ci gaba da kashe wutar, sannan bayan ta lafa ne muka samu gawarwakin mutum biyar a dakin da ke cikin gidan.
Ya ce jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta NEMA sun garzaya da wadanda suka konen zuwa Babban Asibitin Suleja a cikin daren, kuma an sallami amaryar marigayin da karamar ’yarsa karama daga asibiti. Ya ce shi ma kanen marigayin Abdulhadi Maiwada wanda ya fi jikkata, an dawo da shi gida inda ake ci gaba da yi masa jinya irin na gargajiya.
daukacin gidaje biyun dai sun kone tare da kayayyakin da suke ciki.