Gobara ta yi ajalin wani mutum yayin da yake barci a gidansa

An ajiye gawar mutumin a ɗakin ajiye gawa na asibitin Yaba.

Gobara ta yi ajalin wani mutum yayin da yake barci a gidansa

Wani mutum mai suna Obinna ya rasu lokacin da yake barci, bayan da gobara ta tashi a gidansa da ke yankin Iyana-Ipaja a Jihar Legas.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ne, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Ya ce gobarar ta faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 7:30 na dare.

Hundeyin ya bayyana cewa ’yan sanda sun samu kiran gaggawa daga wani mutum game da gobarar.

“Babban jami’in ’yan sanda na yankin ya gaggauta zuwa wajen bayan samun kiran.

“Haka kuma, an sanar da hukumar kashe gobara game da lamarin. Amma, da aka kashe gobarar, an gano wani mutu ya mutu a sanadin gobarar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an ɗauke gawar mamacin zuwa ɗakin ajiye gawa na asibitin Yaba, kafin sanin musababbin tashin gobarar.

Ya ce ’yan sanda na gudanar bincike kan lamarin.

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa